On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Tinubu Ya Ce Ana Yiwa Zabe Mai Zuwa Zagon Kasa

TINUBU

Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Ya ce ya gano wata makarkashiya da ake kullawa domin kawo rudani, wanda zai haddasa dage lokacin gudanar da zaben shugaban kasa da za’a yi ranar 25 ga watan da muke ciki.

Ya yi wannan zargin ne a  yayin gangamin yakin neman zabensa da aka gudanar a birnin Ado Ekiti na jihar Ekiti a ranar juma’a.

Tinubu  ya  ce aniyar wasu  mutane  na kawo  tazgaro  wajen gudanar da zaben  nada manufar ganin an kafa gwamnatin rikon kwarya, sai dai kuma  ya  ce  shirin nasu  ba zai samu nasara ba.

 

Tsohon gwamnan na Legas, ya bukaci  jama’ar kasa  da suyi  tsayuwar  daka tare da kaucewa yin duk wani abu da zai haddasa  tashin zauni tsaye, da kuma tabbatar da cewar suna da katin zabe .

Kalaman Tinubu na zuwa mako daya, Bayan da yayi zargin cewar ana shirin kawo wargaza zabe mai zuwa, ta hanyar amfani da karancin man fetir da kuma sauya fasalin takardun Naira.