On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Tinubu Ya Ce Ya Yafewa Osinabajo

OSINABAJO DA TINUBU

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Ya ce ya yafewa Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Idan ba’a manta ba, Mataimakin shugaban kasar wanda ya kasance  na hannun damar Tinubu, Na daya daga cikin wadanda suka nemi takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar  APC, Wanda daga Tinubu ya samu nasara.

A lokacin da yake jawabi a gaban wata kungiya wadda ta nuna goyon bayanta ga Osinbajo yayin wata ziyara da  ya kawo nan kano a, Dan takarar shugabancin kasar, Asiwaju Tinubu, Yace babu wani ‘kulli tsakaninsa da mataimakin shugaban kasar.

tinubu

Tinubu da Buhari

Ya kara da cewa da kansa yaje har gidansa bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa, Inda  ya kara da cewa mutumin dake neman samun yafiya  daga  Al..h  ya cancanci  ya samu yafiyar.