On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Tinubu Ya Gana Da Shugaban Kanfanin Mai Na Kasa Kan Yadda Za'a Magance Karancin Mai

To a wani mataki na gaggawa da aka dauka domin shawo kan matsalar ta Man fetir, Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da shugaban kanfanin mai na kasa NNPC, Mele Kyari da gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele da sauran manyan mukarraban gamnati a fadar shugaban kasa a ranar Talata.

Kyari ya fadawa   manema labarai bayan taron cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta iya cigaba  da  biyan  tallafin  mai ba, inda ya kara da cewa kamfanin na  bin gwamnatin taraiya  bashin Naira  tiriliyan  2  da  bilyan  8 da aka  yi amfani dasu  wajen biyan tallafin mai a Kasar  nan.

Da yake tabbatar da matsayar shugaban kasar,  Mele  Kyari ya   tabbatar da  cewar, gwamnati  ba zata iya cigaba da biyaan tallafin man  ba,  saboda yana wahalar da kamfanin wajen samar da kudin da za’a yi amfani dasu wajen  biyan tallafin.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati za ta fara daukar matakan dakile illolin cire tallafin  ba  tare da bata lokaci  ba.