On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Tinubu Ya Gana Da Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC

Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu da tsohon sakataren jam’iyyar Iyiola Omisore da suka sauka daga kan kujerunsu, a fadar shugaban kasa dake Villa Abuja.

Mutanen biyu  sun je  fadar shugaban kasar  ne a tare, Kuma  an gansu suna  cikin annushuwa  bayan  kammala  zaman da karfe  1 da rabi na rana,  batare  da sun gana  da manema Labarai ba.

Sai dai rahotanni sun baiyana cewar  ziyarar tasu bata rasa nasaba da  rikicin cikin gida  na jam’iyyar  wanda  yasa  mutanen biyu sauka daga kan mukamansu a makon jiya.

Kazalika  a ranar Litinin din makon jiya an aiyana mataimakin shugaban jam’iyyar  mai kula da shiyyar  Arewa  Sanata Abubakar Kyari a matsayin mukaddashin shugabanta, jim kadan bayan kammala zaman kwamitin gudanarwar  jam’iyyar.