On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Tinubu Ya Jinjinawa 'Yan Najeriya Kan Hakuri Da Yanayin Tsadar Rayuwa

TINUBU

Shugaban kasa Bola Tinubu, Ya taya daukacin al’ummar Musulmi a kasar nan da ma duniya baki daya, murnar sake zagayowar bukukuwan babbar Sallah, Tare da yin kira ga al’ummar Musulmi da su kasance masu yin godiya ga Allah madaukakin sarki da ya ba su damar sake ganin lokacin.

Shugaban  taraiyyar  Najeriyar  ya sauka  filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas   bayan da  ya taso  daga birnin   Landan da misalin karfe 5 da  mintina  13 na yammacin jiya.

A sakonsa na barka  da  Sallah, Shugaban kasar  ya   yabawa ‘yan Najeriya   bisa  hakuri da kuma juriya da suke nunawa  da  yanayin tsadar rayuwa da ake ciki.

Kazalika ya  ce  yana  sane da  irin  kalubalen da jama’a   da jama’a ke  ciki, sai  dai kuma  shi da  masu  dafa masa baya, suna  yin aiki tukuru, domin ganin an magance matsalolin ta  yadda  al’umma zasu amfana.

A cewarsa, yayin da ‘yan Najeriya ke nuna  juriyarsu  da  tsadar  rayuwa  da ake  ciki, dole ne suma  makomarsu  ta kasance  mai farin  ciki, ta yadda  goben  yan Najeriya zata kasance san barka  fiye da yadda ake  ciki a yanzu.