On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Tinubu Ya Roki Kungiyar Kwadago Ta Dakatar Da Shirinta Na Tafiya Yajin Aiki

BOLA TINUBU

shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi kira ga kungiyoyin kwadago das u bashi lokci domin yin duba kan matsalolinsa a maimakon tafiya yajin aiki.

Kakakin majalisar  wakilai,  Tajudden  Abbas ne ya baiyana haka bayan  da  ya jagoranci shugabannin majalisar  damin yiwa  shugaban kasa  jawabi kan tattaunawar da suka yi da kungiyar likitoci masu neman kwarewa  ta kasa, da suka shiga yajin aiki.

Kakakin majalisar  ya Ambato shugaban kasar  na cewar  shi  sabo ne ta  bangaren gudanar da mulkin kasa a saboda  haka  yana bukatar a bashi lokaci  domin yin duba  kan bukatun da ma’aikatan suka bullo das u.

Ya kuma baiyana cewar  suna shirin ganawa  da shugabancin kungiyar kwadago ta kasa  domin rokonsu su kara  bawa  gwamnati lokaci, la’akari da cewar sabuwa ce.