On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tinubu Ya Tafi Kasar Indiya Yayin Da Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Zabensa A Gobe

TINUBU

kuma, kakakin shugaban kasa Ajuri Ngelale ,Ya ce shugaban kasa Bola Tinubu, Bai damu da yadda zata kaya a hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa zata yanke a gobe ba.

A hirarsa da gidan Talabijin na Channels a daren jiya,  Y ace  shugaban kasar  baya  kallon wata barazana dangane da  hukuncin kotun.

Haka zalika ya ce  shugaban kasar  nada kwarin gwiwa  akan hukuncin  da kotun zata yanke, la’akari da kwararran hujjojin da bangarensa ya gabatar.

Bugu da kari  ya ce shugaban kasar  nada kwarin gwiwa ga bangaren  shari’a,  wanda  ya ce  yana da yakinin  za’a sake  tabbatar masa da nasararsa da ya samu.