On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tinubu Ya Yi Maraba Da Hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa

TINUBU

Bayan yanke hukunci da kotun ta yi a daren jiya, Shugaban kasa Bola Tinubu wanda a yanzu haka yake halartar taron kungiyar G20 ta kasashe masu yunkurin habaka tattalin arzikin duniya, ya yi murnar samun nasarar da ya yi a gaban kotun tare da mukarrabansa da suka take masa baya zuwa kasar ta Indiya.

A wani  faifan bidiyo  da  ya karade  shafukan sadarwar zamani,  An nuno  shuguban kasar  ya na  kallon yadda take wakana a zaman kotun kai tsaye  ta hanyar amfani da  Talabijin.

Bayan tabbatar da nasararsa  ta lashe zaben shugaban kasa, Dansa Seyi Tinubu  da sauran mutanen dake   tare dashi, sun ta yashi murnar samun nasara a  kotu.

Daga bisani kuma, Shugaban kasar  ya fitar da wata sanarwa ta hannun Kakakinsa, Ajuri Ngelale,  wanda  ya nuna ya  yi maraba da yadda  hukuncin kotun ya kasance,  yana mai yin kira  da a hada hannu wuri  daya domin gina kasa.