On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tinubu Ya Zabi Godswill Akpabio Da Sanata Barau A Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa Da Mataimaki

Rahotanni na baiyana cewar, Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kammala shirin hada tsohon gwamnan jihar AkwaIbom, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Jibrin Barau daga nan kano a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa

Akpabio da Barau na daga cikin ‘yan takara 9 da za su fafata a zaben shugabancin majalisar dattijai da ake sa ran za a kaddamar a ranar 13 ga watan Yuni.

Majiya mai tushe ta shaida wa jaridar Daily trust  cewa zababben shugaban kasar wanda ya dawo kasar nan a ranar Litinin bayan ya kwashe kwanaki 34 a kasar waje, ya bayyana sha’awarsa ta tsayar da Akpabio da Barau a  matsayin  wanda zasu jagoranci  majalisar dattawa  a  yayin  wani taro da aka yi a Abuja.

A ranar Talata ne tsohon gwamnan jihar Legas ya gana da Sanata  Akpabio  da  Sanata  Barau  sai kuma  Sanata Opeyemi Bamidele na jihar  Ekiti da kuma gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji.

Majiyoyi sun ce, a yayin taron, An bukaci Barau ya janye kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa domin samun hadin kan kasa da kuma  daidaito.