On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Tinubu Zai Halarci Taron Bunkasa Tattalin Arziki Na Duniya A Kasar Saudiyya

TINUBU

A yaune shugaban kasa Bola Tinubu zai ta shi daga Abuja zuwa masarautar kasar Netherland domin yin wata ziyarar aiki.

Wata sanarwa da kakakinsa  Ajuri Ngelale  ya fitar, ta baiyana cewar  shugaban kasar  zai kuma halarci  taron majalisar bunkasa tattalin arziki ta duniya, wanda  za’a yi ranar  28 zuwa  29 ga watan da muke  ciki a kasar  Saudiyya.

Sanarwar  ta kara  da cewar,  Gaiyattar  da Firiyiministan kasar Netherland  Mark  Rutte  ya yiwa  shugaban kasa Bola  Tinubu, za taba muhimman batutuwan samar da cigaba, sannan kuma  zai gana da sarki Willem  Aleander  da sarauniya  Maxima ta masarautar.

Kazalika shugaban kasar zai  halarci  taron  ‘yan  Najeriya dake gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari a kasar ta Netherland , wanda  zai tattauna  kan hanyoyin da kasashen biyu  zasu ci gajiyar  juna  ta bangaren yin kawance, musamman aikin gona da kuma sarrafa albarkatun ruwa da ake da  su.