On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tinubu Zai Kirkiri Wasu Sabbin Ma'aikatu

TINUBU

Alamu na nuni da cewar shugaban kasa Bola Tinubu zai kirkiri wasu sabbin ma’aikatu daga cikin wadanda ake dasu,Kamar yadda shugaban ma’aikatansa Femi Gbajabiamila ya baiyana a daren jiya a Abuja.

Gbajabiamila  ya  ce  shugaban kasar  na son ya baiwa  kowacce  ma’aikata  yancin gashin kanta .

A yanhaka dai an  fara tura  zagayen farko na sunayen mutanen da ake son nadawa kan matsayin ministoci a  jiya ga  zauren majalisar  dattawa .  Yayin da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar,  ya  baiyana  cewar   za’a  tura  ragowar  sunayen mutane  13  da za’a  nada kan matsayin ministoci  ga majalisar  dattawan  nan bada jimabawa  ba.

Ya kuma baiyana cewar  daga cikin sunayen babu  wanda  aka  nuna ma’aikatar  da zai  yi aiki a cikinta,  wanda  manufar  yin hakan shine baiwa  majalisar  damar  yin nazari na tsanaki akan sunayen da aka tura mata.