On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tinubu Zai Tura Sunayen Ministoci Ga Majalisa

BOLA TINUBU

Matukar ba wani sauyi aka samu ba, Rahotanni na baiyana cewar shugaban kasa, Bola Tinubu zai aike da sunayen mutanen da yake son nadawa a matsayin ministoci a gwamnatinsa, da zarar an kammala hutun babbar sallah, ga majalisar dokoki ta kasa domin tantancewa.

A yaune  ake saran shugaban kasar  zai dawo  gida Najeriya da birnin Landan, inda zai wuce  zuwa birnin Ikko domin yin idin babbar sallah.

Shugaban kasar  ya zarce zuwa Burtaniya daga kasar Faransa inda  ya halarci  taron tafiyar da harkokin kudi na duniya, wanda  shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya karbi bakuncin taron.

Jaridar Punch  ta Ambato wata majiya na baiyana cewar,  kusan  an kammala rubuta sunayen  ministocin da  Tinubun zai nada a gwamnatinsa,  inda za’a tura su majalisa domin tantancewa  bayan hutun babbar sallah.