On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Tsadar Rayuwa Tasa Iyayen Dalibai A Kano Na Shakkun Komawarsu Yaransu Makaranta

GWAMNA GANDUJE

Jama’ar Kano sun baiyana rashin tabbacin da suke dashi na yin shirin da ya dace domin komar da yaransu makaranta a sabon zangon karatu na shekarar 2022 zuwa 2023.

Wasu daga cikin iyayen yara da suka zanta da wakiliyarmu Joy Godson sun baiyana gazawarsu na yin shirin da ya dace domin mayar da yaransu  makaranta a sakamakon tsadar rayuwa da ake ciki.

Da suke baiyana halin matsi da ake ciki, Iyayen Yaran  sun baiyana kalubalen rayuwa da ake ciki a matsayin dalilan da suka sa basu da tabbacin mayar da yaransu makaranta a sabon zangon karatu mai kamawa.

Kazalika sun baiyana cewa kamata yayi a dage  lokacin komawa sabon zangon karatun wanda zai fara daga ranar  13 ga watan da muke ciki, domin basu lokaci da zasu kimtsa yadda yadda  ya kamata

More from Labarai