On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Tsagin Gwamnonin PDP 'Yan G-5 Sun Bukaci Tinubu Ya Goyawa 'Yan Takararsu Baya, Kafin Su Mara Masa Baya

GWAMNONIN PDP YAN G-5

Tsagin Gwamnonin jam’iyyar PDP biyar da suka shata layi da jam’iyyar, Sun bukaci Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da ya goyi bayan ‘yan takararsu na gwamna sanatoci a jihohin da suke.

Rahotanni na baiyana cewa,  Daga cikin sharuddan da  gwamnonin masu inkiyar  G-5 suka gabatar wa Tinubu yayin ganawarsu a  birnin Landan na kasar Birtaniya a ranar Talata, shine zai nuna goyon bayansa ga  ‘yan takararsu na gwamnoni da  sanatoci na jam’iyyar  PDP a jihohin da suke.

Tawagar  gwamnonin ta kunshi wadansu   tsaffin  gwamnoni da suka hada  Donald Duke  sau   Jonah Jang da  Olusegun Mimiko, ,da kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Cif Bode George.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa gwamnonin biyar sun damu da yadda makomarsu ta siyasa zata kasance  yayin da suke cigaba da kamun kafa a wajen Tinubun.