On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tsoffin Daliban FGC Sun Gudanar da Zanga-Zanga Lokacin da Ministan Ilimi ke Shiga Makarantar

Kungiyar Tsofaffin Daliban Kwalejin Tarayya ta Kano (FGCOSA), ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta mutunta umarnin kotu da ya umarci bangarorin da ke rikici su cigaba da kasancewa yadda suke har sai an yanke hukunci kan shirin cefanar da wasu filayen makarantar.

Shugaban kungiyar reshen Kano, Farouk Aminu Bawa, ya yi wannan kira ne a yayin wata zanga-zangar lumana da kungiyar ta gudanar a harabar makarantar ranar Lahadi, lokacin da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ziyarci makarantar.

Da yake magana da Arewa Radio, Bawa ya ce manufar zanga-zangar ita ce jawo hankalin Ministan Ilimi da ya sake nazarin shirin cefanar da wani bangare na filin makarantar karkashin tsarin haÉ—in gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP).

Ya ce kungiyar na ganin matakin zai yi illa ga yanayin koyarwa da kuma cigaban makarantar nan gaba.

Ya bayyana cewa kungiyar ba ta adawa da cigaban makarantar ko shigar masu zaman kansu wajen samar da ababen more rayuwa, sai dai tana adawa da duk wani tsari da zai rage filin makarantar ko kuma ya jefa makomar cibiyar ilimin cikin hadari.

Bawa ya kara da cewa kotu zata cigaba da sauraren wannan shari'a a ranar 26 ga Agustan 2026, yana mai bayyana fatan cewa zanga-zangar lumanar za ta bude kofar tattaunawa tsakanin kungiyar da Gwamnatin Tarayya domin cimma mafita mai dorewa.

Rikicin ya samo asali ne daga shirin gwamnatin tarayya na aiwatar da wani aikin hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu, wanda ya hada da mika kusan hekta 30 zuwa 33 na filin makarantar domin gina sabbin kayayyakin more rayuwa.

Tsofaffin daliban sun ce ba a tuntube su yadda ya kamata ba kafin daukar matakin, yayin da suke ganin filin da aka ware yana da muhimmanci ga fadada makarantar da kuma ayyukan ilimi a nan gaba.

A baya, kungiyar ta gudanar da zanga-zanga tare da hadin gwiwar Kungiyar Tsofaffin Daliban Unity Schools ta Kasa (USOSA), inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta soke shirin tare da kare filayen makarantun hadin kan kasa daga abin da suka bayyana a matsayin amfani da su wajen kasuwanci.

 

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 35°C | Low: 23°C