On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tsohon Gwamnan Bankin Kasa Zai Yi Bukin Kiristimeti Da Sabuwar Shekara A Gidan Gyaran Hali Na Kuje

Tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, zai yi bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara a gidan gyaran hali na Kuje.

Hakan ya faru ne saboda  kasa cika sharuddan bada belinsa da  ya  yi  a  ranar Talata. Bayan zaman kotun a jiya jami’an hukumar gidan  gyaran halin  sun  sake  tafiya  da Emefiele.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC Na zargin  Emefiele da aikata lefuka  guda shida da suka hada da saba yarjejeniyar bada  kwangila ga wani kanfanin zuba jari, da kuma  yin almundahanar kudi.