On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na’Abba ya rasu.

Da safiyar Larabar nan ne shugaban majalisar ta 8 ya rasu a Abuja.

Ko da yake har yanzu babu cikakken bayanai kan rasuwarsa, majiyoyi sun ce za a yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Abuja.

An haifi Na’Abba a ranar 27 ga watan Satumba, shekarar 1958.

Marigayi Ghali Na'Abba masanin kimiyyar siyasa ne kuma mai tsara manufofi.

Ya shiga jam’iyyar PDP ne a shekarar 1998 a lokacin kafuwarta.

Ya zama dan takarar jam’iyyar ne a watan Afrilun 1999 a zaben majalisar dokokin tarayya a mazabar birnin da kewaye, kuma ya lashe zaben majalisar wakilai.

Bayan  samun nasara da goyon bayan sauran zababbun ‘yan majalisar wakilai daga shiyyar Kano da Arewa maso Yamma, ya zama shugaban majalisar wakilai.

Ya taba rike matsayin shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar.