On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Tsohon Mataimakin Gwamna A Jihar Nasarawa Ya Shaki Iskar 'Yanci

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfesa Onje Wado da aka yi garkuwa da shi a yanzu ya kubuta.

Wado, wanda aka yi garkuwa da shi daga gidansa da ke Rinza a daren ranar Alhamis, ya kubuta ne bayan ya biya Naira miliyan 4 a matsayin kudin fansa.

Wata majiya daga danginsa ta ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 70, amma dangin sun tattauna kuma a karshe suka biya Naira miliyan 4 kafin a sako shi.

Shima wani tsohon kwamishinan yada labarai a jihar  Dogo Shamma ya tabbatar da sakin Farfesa  a daren jiya.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 37°C | Low: 23°C