On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Tsohon Ministan Raya Yankin Naija Delta Ya fice Daga Jam'iyyar PDP

Tsohon Ministan Raya Yankin Naija Delta

Tsohon ministan yankin Neja Delta, GodsDay Orubeebe Ya fice daga jam’iyyare PDP, Sakamakon Abunda ya baiyana na rashin aiwatar da tsarin Dimukuradiyya.

Cikin  wata  wasika  daya  aikewa  shugaban  jam’iyyar  na  kasa ,Iyorchia  Ayu,  mai  dauke  da  kwanan  watan  yau  Litinin 20  ga  watan  da  muke ciki,  cikin  wasikar  Orubebe  ya shaida  cewa   ficewa  daga  jam’iyyar  batare  da  bata  Lokaci  ba  kuma  ya  sanar  da   shugaban   mazabarsa    a  karamar  Hukumar  Buturu  a  jihar  Delta

Orubebe  ya  kuma nuna  damuwa  kan  Gazawar  jam’iyyar  wajen kin  amfani  da  tsarin  karba-karba  wajen  bada  tikitin   takarar  shugaban  kasa,  yana  mai cewa  bashi  da  niyyar  sake  karbar  wani  mukami  daga  gwamnatin  shugaban  kasa  buhari  a  shekarar 2023

Tsohon ministan ya kuma bayyana cewa halin da jam’iyyar PDP ke ciki a yanzu bai nuna cewa jam’iyyar a shirye take ta kwato mulki a zaben 2023 ba.

More from Labarai