On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tsohon Ministan Shari'a Ya Musanta Cewar Ya Gudu Daga Najeriya

MALAMI

Tsohon Ministan Shari’a na kasa, Abubakar Malami ya musanta rahotannin dake cewar ya cika wandonsa da iska, saboda zarginsa da aikata lefukan cin hanci.

Biyo bayan dakatarwar da aka yiwa shugaban hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, An samu wasu rahotanni dake  baiyaana cewar,  Tsohon ministan shari’ar  ya fice daga kasar nan, domin kaucewa yunkurin kama shi  tare da yi masa bincike.

Wata majiya daga hukumar EFCC, ta  fadawa jaridar Daily trust cewar, Hukumar EFCC  na bukatar samun bayanai  daga wajen Abubakar Malami kan zarginsa da hannu, wajen siyar da wata gangar danyen milyan 48 ta  barauniyar  hanya, akan kudi Dala Bilyan 2 da milyan 400 a shekarar  2015.

Majiyar  ta  ce  hukumar ta gaiyaci  tsohon ministar shari’ar  na kasa, to sai  yaki amsa gaiyatar da hukumar ta yi masa.

To sai Malamin ya musanta rahotannin dake cewar baya  Najeriya, Inda  ya  baiyana cewar yau juma’a zai halarci wani daurin aure a masallacin Marigayi Sheik Isyaka Rabiu dake nan kano da karfe 2 na rana.