On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Tsohon Sakataren Gwamnatin Taraiyya Babachir David Ya Caccaki Bola Tinubu Kan Zaben Shettima A Matsayin Mataimakinsa

Tinubu Da Babachir

Tsohon Sakataren Gwmanatin Taraiyya, Engr. Babachir David Lawal, Yayi fatali da matakin aiyana Kashim Shettima a matsayin Dan takarar Mataimakin shugaban kasa, na jam’iyyar APC mai mulkin kasa zabe mai zuwa.

A ranar Lahadin data gabata ce, Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya aiyana kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimaiki, al’amarin da  ya dumama  musayar ra’ayi a tsakanin al’umma.

Kazalika shima  Babachir David Lawal,m wanda ya kasance mai goyon bayan Tinubu, Yayi  tir da matakin da Dan takarar shugaban kasar ya dauka.

Wata sanarwa  da  ya fitar a daren jiya, Tsohon sakataren gwamnatin taraiyyar, Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari  da  yayi amfani da karfin ikonsa na kwamandan Askarawan Najeriya da kuma kasancewarsa jagoran jam’iyyar APC na kasa, wajen soke nadin da aka yi.