A yau ne aka cika shekara daya da rasuwar tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a birnin London na kasar Birtaniya a ranar 13 ga Yulin 2025 yana da shekaru 82 a duniya bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.
An yi jana'izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci a garinsu na Daura da ke Jihar Katsina a ranar 15 ga Yulin 2025.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da manyan jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya da dubban masu jimami ne suka halarci jana'izarsa bayan an dawo da gawarsa Najeriya.
Buhari ya kasance Shugaban Mulkin Soja na Najeriya daga shekarar 1983 zuwa 1985, sannan ya zama zababben Shugaban Kasa daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Comments
Add a comment