On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tsohon Shugaban Kasar Sri Lanka Gotabaya Rajapska Na Shirin Komawa Gida Bayan Ya Tsere Daga Kasar.

GOTABAYA RAJAPASKA

Ana sa ran tsohon shugaban kasar Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa zai dawo kasar daga Singapore.

Kakakin majalisar ministocin kasar Bandula Gunawardena ya fadawa  manema labarai a ranar Talata cewa Mista Rajapaksa  bai boye kansa a wani wuri ba, kuma zai iya dawowa gida kowane lokaci daga yanzu.

Tsohon shugaban  kasar  ya tsere daga kasar Sri Lanka bayan tarzomar da ta barke a kasar saboda tabarbarewar tattalin arziki.Da yawa daga cikin masu zanga-zangar sun ce ya karkatar da akalar kudaden kasar, lamarin da ya janyo tashin farashin kayayyakin masarufi.

Mista Rajapaksa ya bar Sri Lanka a ranar 13 ga Yuli zuwa Maldives, kafin ya wuce zuwa Singapore a ranar 14 ga Yuli.

 

 

More from Labarai