On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Victor Oshimhen Ya Shiga Cikin Jerin Masu Takarar Ballon d’Or

VICTOR OSHIMHEN

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta taya dan wasan Super Eagles Victor Osimhen murnar saka sunansa cikin jerin masun neman kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d’Or ta shekarar 2023.

'Yan  wasa  30 ne  ke takarar  gwarzon  dan  wasa  ta   Ballon d'Or, wand a suka  hada da  Lionel Messi da  Erling Haaland sai  Kylian Mbappe da dai sauransu.

A sanarwar da hukumar  CAF ta fitar, ta taya Osimhen da Andrey Onana da  Yassine Bounou da  Mohammed Salah murnar kasancewarsu a cikin jerin yan wasan.

Osimhen ya taka rawar gani a kakar wasan da ta wuce kuma ya zura kwallaye uku a wasanni uku da ya buga a gasar Seria A ta  bana. A yanzu haka yana tare da Super Eagles yayin da suke shirin tunkarar gasar neman gurbin shiga gasar AFCON da kasar  Sao Tome da Principe a wasan da zasu yi  ranar Lahadi.

Haka zalika  itama  Tauraruwar Super Falcons, Asisat Oshoala An saka ta cikin jerin masu  takarar  gwarzuwar  yar wasa  ta   Ballon d’Or a  bangaren   mata na shekarar 2023.