On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Wajibi Ne Masu Motoci Da Shaguna Su Samar Da Mazubin Shara A Wajensu Daga 1 Ga Watan Yuni

Sabon gwamnan jihar Kano,Ya bada umarnin cewar daga ranar 1 ga watan gobe na Yuni,Ya zama wajibi dukkanin wasu motoci dake bin titinan jihar kano da kuma Shagunan siyar da kayayyaki, su kasance suna da kwandon zuba shara a wurarensu, domin tabbatar da tsaftace jihar kano.

Domin tabbatar da wannan  kudiri,  Gwamnan na Kano, Abba Kabir  Yusuf, Ya yi alkawarin kafa kwamitin kartakwana kan kwashe  shara  da  yashe magudanan  ruwa  da  kuma  tsaftace  hanyoyi, mai taken, Operation Nazafa.

Ya ce  nan da  ‘yan kwanaki masu zuwa zai  kaddamar da gangamin  tare da kungiyoyin  temakon kai da kai  domin  tabbatar da  aikin na kwamitin kartakwana.

Bugu da kari  yayi alkawarin kwashe  dukkanin wata tarin  shara  da aka zubar   tare da yashe  magudanan ruwa  nan da  ‘yan makwanni masu zuwa,  da kuma tabbatar da  samar da dorarren  tsarin kula das u da kuma tsaftace su.