On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wanene Zai Maye Gurbin Sanata Abdullahi Adamu A Jam'iyyar APC Ta Najeriya ?

Wasu rahotonni da ba a tabbatar ba na nuni da cewa akwai yiwuwar tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje zai maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Bayanan sunce shugaba Bola Tinubu yana nazarin neman a baiwa  Ganduje shugabancin APC domin  maye gurbin Adamu.

Rahotanni a daren jiya na cewa an cire sunan Ganduaje daga jerin sunayen ministocin Tinubu kuma majiyoyi sun nuna cewa Tinubu ya gamsu sosai da zabin Ganduje.

Zamu kawo muku karin bayani  akan batun.