On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Wani Basarake Ya Mutu A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar Kogi

Wani basaraken gargajiya na yankin Aghara dake karamar Hukumar Kabba Bunu a jihar Kogi mai suna Chief David Obadofin da aka yi garkuwa dashi, Ya mutu a hannun masu garkuwar.

Rahotanni sun baiyana cewar basaraken ya mutu ne a ranar  Alhamis din data  gabata  bayan shafe  kwanaki 12 yana a hannunsu,Inda  ta kaiga ko tsayawa  baya iya  yi,sakamakon U’kubar da  masu garkuwar suka gana masa.

Basaraken wanda ya kasance babban manomin Yazawa a yankin, Anyi awon gaba dashi ne a lokacin da ake bukukuwan  Easter  da karfe  11 na dare  lokacin da yake  cikin wani gidan gonarsa.

Rahotanni sun baiyana cewar yan bindigar sun amince su karbi naira milyan 2 lokacin da suka fahimci basaraken na  halin gargara, kafin su sakeshi tare da  wata mai suna Temidayo.

Daga karshe macen ta kubuta a hannunsu a  yayin das hi kuma  rai yayi halinsa kafin a kaiga biyan kudin fansar,  Kazalika  Masu garkuwar  sun bindige  wata bazawara mai suna Toyin Onare  wadda  ta kasance ma’aikaciya a gidan gonar.