On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wani Bene Mai Hawa 7 Ya Rufta A Jihar Legas

LEGAS

Wani Bene mai hawa bakwai da ake kan aikin gina shi a yankin Banana Island dake birnin Ikko ya ruguje, wanda hakan yayi sanadin makalewar ma’aikata da dama a cikin baraguzan ginin.

Jami’in Hukumar bada agajin gaggawa  ta kasa  reshen jihar  Legas shine  ya tabbatar da faruwar  abun alhinin a ranar  Laraba,lokacin da yake  ganawa da manema Labarai.

Bugu da kari  shima kakakin Ma’aikatar Kasa da tsare-tsarenta  ta  jihar  Legas, Munkaila Sanusi ya  tabbatar da cewar  ba’a samu  asarar  rai ba, inda  banda  wadanda  suka samu  raunika  da ake  kan  dubasu  yanzu  haka.

Ya  kara  da cewar  Benen da ake kan aikin ginawa  bai samu amincewa  daga hukumomin da suka  kamata  ba.