On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Wani Mai Babur din Adaidaita Sahu Ya Halaka Wani Mutum Har Lahira Ta Hanyar Caka Masa Almakashi

Kakakin Rundunar Yansandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna kiyawa.

Rundunar Yansandan jihar Kano ta tabbatar da kisan gillar da aka yiwa wani mai suna Abdulrrahma Usman a Panshekara Wanda Wani Dan Adaidaita sahu da ba’a kaiga tantacewa ba Ya aikata

Wakilinmu Bashir  Faruk Durumin Iya, Wanda ya ziyarci yankin ya ruwaito mana cewa, Mai Babur din Adaidaita Sahun  ya dabawa Marigayin Almakashi ne da karfe 9 na dare  kafin daga bisani ya cika wandonsa da Iska.

Wani  ganau wanda ya kasance abokin Marigayin mai suna Aliyu Muhammad, Yayi karin haske  kan yadda aka halaka abokin nasa, wanda aka bari cikin jini male-male  bayan sa’in sar  data kaure a tsakaninsu.

 Kazalika  shima  kakakin  Rundunar  yansandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa  ya  tabbatar da faruwar  lamarnin.

 

 

 

 

More from Labarai