On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Wani Matashi Mai Damfarar Maza Da Sunan Mace A Shafukan Sada Zumunta Ya Fada Komar Yansanda.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Rundunar Yansandan jihar Kano,Ta Cafke Matashin Mai Suna Musa Maje, da ake Tuhuma da Damfarar Maza ta hanyar amfani da Sunan Mace a shafukan Sada zumunta.

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta kama Wani Matashi mai suna Musa Maje da ake zargi da kirkirar Shafukan Sada Zumunta Mai Sunan 'Yan Mata, inda ake zargin sa da damfarar mutane da dama.

'Daya daga cikin Shafin dayake amfani dashi akwai mai Suna Zahra Mansur.

Jami'in Yada Labaran Rundunar 'Yansan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fidda wannan Labari tare da bada wadannan Lambobin Waya dan Kiran Hukumar muddin ka taba fadawa tarkonsa 08067060267 ko 08065060100.

 

Kiyawa

More from Labarai