On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Wani Matashi Ya Gamu Da Ajalinsa Sakamakon Nutsewa Cikin Kududdufi A Kano

KUDUDDUFI

Wani matashi dan shekara 17 a duniya mai suna Suleiman Muhammed, ya nutse a cikin wani kududdufi dake unguwar Wailari ta karamar hukumar Kumbotso a nan jihar Kano.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Laraba a nan  Kanon dabo, Yace lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

Kakakin hukumar ya ce an fito da matashin daga cikin  ruwan a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

 Ya kuma baiyana cewa  lamarin ya samo asali ne bayan da matashin yace  kududdufin domin yin ninkaya.

Abdullahi ya ce an mika gawar  marigayin ga mai unguwar  Wailari Magaji Adamu inda aka yi masa sutura.