On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wani Matashi Ya Sace Wani Yaro Tare Da Halaka Shi Har Lahira A Nan Kano

Garkuwa da Mutane

Jami’an yansanda a nan Kano sun kama wani Matashi dan shekara 29 a duniya mai suna Ado Ibrahim, Sakamakon zarginsa da aikata lefin yin garkuwa da wani yaro dan shekara Biyar a duniya mai suna Hamza Harisu, kuma ya halaka shi har lahira, Sannan kuma daga bisani ya nemi a biyashi naira milyan 20 a matsayin kudin fansa.

Da yake tabbatar da kamen, kakakin rundunar yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, Ya ce an kama Ado ne tare da wasu mutane ukku da ake zargi.

Kiyawa ya kara da cewa, Mahaifin yaron ne ya kai rahoton al’amarin ga rundunar yansandan jihar  Kano, wanda ya faru a karamar hukumar Doguwa ta nan jihar kano , Kuma matakin gaggawa da aka dauka yasa aka dakume wanda ake zargin tare da abokan burminsa.

Ya ce a lokacin da ake yima tambayoyi, Gogarman masu aikata lefin, ya tabbatar da cewa ya sace yaron a ranar 27 ga watan da ya gabata, da karfe 7 na yammaci, Sannan kuma ya yaudare shi zuwa wani Daji, yayin daga bisani ya halaka shi har  lahira.