On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Wani Rahoto Ya Nuna Cewa An Kai Hari Sansanonin Soji 16 Cikin Watanni 18 A Sassan Najeriya.

Ya zuwa yanzu 'yan ta'adda da suka addabai sasam kasar sun kai hari kusan sansanonin soji 16 a cikin watanni 18 da suka gabata, al’amarin da ya kara haifar da fargabar cewa maharan sunfi karfin dakarun sojoji kuma ana bukatar sake bijiro da wasu dabaru don tunkarar masu laifin.

Bincike ya nuna cewa yayin da wasu hare-haren suka kai ga kashe sojoji, an fatattaki wasu ‘yan bindigar tare da kashe maharan.

Har ila yau, anrawairo cewa a cikin watanni biyun da suka gabata, an kashe sojoji sama da 800 a sassa daban-daban na kasarnan.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, ya bayyana cewa ba za a amince da yawan hare-haren da ake kaiwa ‘yan Najeriya ba, yana mai zargin wasu ‘yan kasashen waje da rura wutar matsalar tsaro a kasar.

A halin da ake ciki, Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki  sojojin haya domin  magance matsalar rashin tsaro.