Al'umar yankin Lata Nna dake karamar hukumar Patigi ta jihar Kwara sun rubutawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wasikar neman daukin gaggawa akan matsalolin garkuwa da mutane, yanta'adda da kuma kashe-kashe da ya addabi su.
Al'ummar sun kbukaci Shugaba Tinubu ya ba da umarnin kaddamar da cigaba da gudanar da ayyukan tsaro domin fatattakar 'yan bindiga daga maboyarsu da ke kewaye da yankin.
Sun kuma bukaci a ba iyalan wadanda suka rasa rayukansu tallafi tare da tabbatar musu da adalci, musamman iyalan Alhassan Ndaba da mazauna biyu da aka kashe a ranar 26 ga Yunin 2026.
A cewar al'ummar, "Mai Girma Shugaban Kasa, mun zabi gwamnati ne da fatan samun tsaro da rayuwa mai inganci. Don Allah kada ku bari a shafe garin Lata Nna daga taswira. Ku ji kukanmu, ku kawo mana dauki."
Sun ce tsawon shekaru biyu kenan suna fama da hare-haren 'yan bindiga ba tare da gwamnati ta daukia matakin da ya dace ba.
"Mun sha fama da sace mutane, karbar kudin fansa, mamaye gonaki da kuma fashi da makami cikin shiru. Amma hare-haren da za mu lissafo su ne suka jawo hankalin jama'a saboda girman barnar da suka yi da kuma irin danyen aikin da aka aikata."
Sun ce a watan Agustan shekarar 2025, mafarauta 65 sun rasa rayukansu a daji yayin artabu da 'yan bindiga, sakamakon amfani da makamai marasa karfi da mafarautan ke yi, yayin da 'yan bindigar ke dauke da manyan makamai irin su AK-47 da makamantansu, inda gawarwaki 40 kacal aka samu aka binne.
Sun kuma ce a ranar 15 ga Afrilun 2026, an kashe Alhassan Ndaba ta hanyar mugunta yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gona domin neman abin ciyar da iyalansa.
A cewarsu, a ranar 10 ga Yulin 2026, 'yan bindiga sun kutsa cikin garin Lata Nna da rana tsaka, suna shiga gida-gida inda suka kwashe kayan abinci, kudi da wayoyin hannu, tare da fasa shaguna suka sace kayayyaki, sannan suka tafi da babura hudu da kudinsu ya kai Naira miliyan 1.6, lamarin da ya nakasa zirga-zirga da sana'o'in matasa.
Sun kara da cewa a ranar 13 ga Yunin 2026, wasu 'yan bindiga hudu dauke da makamai, suna kan babura biyu, sun shiga garin da rana tsaka suna yawo ba tare da tsoro ba suna neman katin waya, fetur da sauran kayayyaki, abin da ya jefa daukacin al'umma cikin firgici.
Al'ummar sun bayyana cewa ranar 26 ga Yunin 2026 ita ce mafi muni a tarihinsu, bayan da 'yan bindiga suka tare hanya daya tilo da ke shiga da fita daga garin, wanda ita ce hanyar zuwa asibiti, kasuwa da samun agaji, inda suka kashe mazauna biyu da ke dawowa gida.
Sun kuma ce a ranar 27 ga Yunin 2026, wasu mazauna da suka je debo ganyayyaki a bayan kauyen an tare su da bindiga tare da kwace wayoyinsu da kudinsu.
A karshe, sun ce a ranar 15 ga Yulin 2026, wasu 'yan bindiga sun yi wa wani mai sana'ar POS fashi da makami bayan ya dawo daga banki da kudin gudanar da kasuwancinsa, inda suka kwace masa dukkan kudin da yake dauke da su.
Comments
Add a comment