On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Wasu Dalibai Hudu Da suka Kammala Jarabawar WAEC Sun Mutu Bayan Sunje Wanka Gabar Teku A Jihar Legas

GABAR TEKU

Wani abun alhini ya faru a gefen gabar tekun Elegushi da ke unguwar Lekki a jihar Legas, bayan da wasu matsakaitan matasa hudu suka nutse cikin ruwa a lokacin da suke tsakaya da yin ninkaya a wajen.

Matasan wadanda  basu jima  da kammala kwalejin  Kuramo dake  yankin na Lekki ba, sun je yin iyo ne a  bakin ruwan domin murnar kammala rubuta  jarrabawar  WAEC lokacin da lamarin ya faru.

Mai magana da yawun hukumar kula da gabar  tekun Elegushi, Cif Ayuba Elegushi, a ya ce Daliban basu bi ka’idar  data dace  wajen yin ninkayar ba.

Ya kara  da  cewa abun ya faru ne a wani waje  da  ba’a barin mutane suje domin yin wanka a gabar  tekun.

A wani bangaren kuma, wani Mai Babur mai kafa biyu ya rasa ransa sakamakon  wata  arangama tsakanin Yan Acaba   da ‘yan sanda kan wani hatsarin da  ya  faru a unguwar Abule-Egba da ke jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata  ta cikin wani sako daya  wallafa a shafinsa na Twitter.

Sai dai kuma yace an samu lafawar kura  bayan da aka tura jami'an yansanda wajen da abun ya faru.