On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Wasu 'Yan APC Sun Gamu Da Ajalinsu Akan Hanyarsu Ta Zuwa Abuja Daga Imo

APC

Gabanin rantsar da zauren majalisar dokokin kasa na goma a yau, Wasu ‘yan jam’iyyar APC da suka taso daga jihar Imo,domin halartar bukin rantsuwar sun gamu da ajalinsu, sakamakon hadari da suka yi.

Kakakin jam’iyyar  APC  a jihar Imo,  Cajetan Duke  ya  tabbatar da faruwar abun alhinin,  inda  ya baiyana cewar motar da  mutanen ke ciki  ta yi karo da wata  motar Bas a jihar Delta.

Ya  tabbatar da mutuwar mutane biyu a yayin da wasu suka ji raunika ,  inda aka garzaya dasu Asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Mai magana da yawun jam’iyyar ta Apc  Ya lamarin a matsayin mai sosa zuciya.