On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wasu 'Yan Siyasa Na Shirin Kera Na'urar Tantance Masu Zabe Domin Yin Magudin Zabe Inji INEC

NA'URAR TANTACE MASU YIN ZABE TA BVAS

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, ta ce, ta gano kullin da wasu ‘yan siyasa ke yi na kera na’urar tantance masu zabe ta zamani BVAS, domin yin magudi a zaben shekara mai zuwa.

Shugaban sashin wayar da kan masu zabe na hukumar, Achumie Rex ne ya baiyana haka a ranar Laraba, a yayin da yake jawabi a wajen wani  taron karawa juna sani na yini biyu da aka shiryawa kungiyoyin farar hula, akan kada kuri’a.

Ya kara da cewa  wasu daga cikin yan siyasar  na kokarin yin kutse a babban  rumbun ajiyar bayanan hukumar  dake kan internet  gabanin babban zaben kasar nan dake tafe,  ya kuma kara da cewa  hukumar  ta dauki dukkanin matakan da suka dace, domin dakile yunkurin ‘yan siyasar.

Daga nan sai ya sake jaddada yunkurin hukumar zabe ta kasa INEC, na gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa.