On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Wasu 'Yan Siyasa Sunyi Yunkurin Kafa Gwamnatin Rikon Kwarya A Najeriya Inji DSS

DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar da cewar wasu manyan yan siyasa da bata baiyana sunayensu ba, sunyi yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya a Najeriya, inda ta bayyana shirin a matsayin wanda bai dace ba.

A cewar hukumar, shirin zai gurgunta mulkin farar hula tare da jefa kasar nan cikin wani mawuyacin hali.

Bayanin hakan na kunshe  ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Peter Afunanya ya fitar ranar Laraba.

Hukumar ta DSS ta yi kakkausan gargadi ga masu shirin dakile tsarin  dimokuradiyya a kasar nan da su  gaggauta  janye makarkashiyar da suke yi ko kuma su fuskanci fushin hukuma.