On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wata Babbar Mota Ta yi Ajalin Mutum 17 A Titin Bauchi Zuwa Jos

Mutum kusan 20 ne aka tabbatar sun rasu sakamakon wani hatsarin mota a kan babbar hanyar Bauchi zuwa birnin Jos na Jihar Filato.

Wani ganau yace hatsarin ya ritsa da babbar mota wato tirela ɗaya wadda ta murƙushe ababen hawa kusan 10.

"Mun ƙirga baburan a-daidaita-sahu uku da kuma mota bakwai da motar ta murƙushe," a cewar Sani Babale.

Ya ƙara da cewa zuwa lokacin da yake magana sun ƙirga gawar mutum 17 da hatsarin ya yi ajalinsu.

"Mutum biyar ne suka rasu nan take, sai kuma aka kai bakwai asibiti. Ɗazu ma aka yi jana'izar wani yaro. Daga baya dai mun ƙirga gawar mutum 17."

Anata bangaren hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa reshen Jihar Filato ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa direban motar ne ya gaza sarrafa ta sakamakon farfelar motar da ta fice daga jikinta.

Sai dai sanarwar da Alphonso Godwin ya saka wa hannu ta ce mutum 10 ne suka mutu tare da jikkata wasu 15.