Wata malamar makaranta kuma marubuciya a Jihar Kano, Hajara Namadi Imam, ta kaddamar da wani littafin koyo da ya haɗa Hausa da Turanci da Larabci domin inganta koyarwa da harshen uwa, ƙarfafa al'adar karatu da bunƙasa ilimi a matakin al'umma.
Littafin, wanda ta shafe shekara uku tana gudanar da bincike da nazarin harsuna kafin kammala shi, an tsara shi ne domin sauƙaƙa koyon harsuna, inganta karatu da rubutu, tare da taimaka wa yara wajen haɓaka ƙwarewar sadarwa ta hanyar koyon harshen uwa da kuma harsunan ƙasa da ƙasa.
Da take jawabi a wajen ƙaddamar da littafin a Makarantar Madina International School da ke Yankusa a Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hajara Namadi Imam ta yi kira da a ƙara ƙarfafa al'adar karatu a tsakanin al'umma.
Da yake wakiltar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Ali Musa Danmaliki, Sakataren Ƙaramar Hukumar, Kabir Nasir, ya ce wannan littafi ya yi daidai da ƙudirin gwamnati na inganta ilimi ta hanyar samar da sabbin hanyoyin koyarwa da kayan koyo.
Comments
Add a comment