On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ya Kamata Sabuwar Gwamnati Ta Dauki Darasi Daga Kura-Kuran Da Gwamnatocin Baya Suka Tafka

SANUSI NA BIYU

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya shawarci gwamnati mai jiran gado da ta dauki darasi daga kura-kuran gwamnatocin da suka shude suka yi, ta hanyar nada kwararrun mutane a mukamai da za su bunkasa cigaban kasa.

Da yake jawabi a yayin taron kaddamar da  wani  littafi  a  Abuja ranar Talata, Malam Muhammadu Sanusi ya ce yana fatan ganin jerin sunayen ministocin da shugaban kasa  mai jiran gado  zai nada.

Ya kuma yi kira ga gwamnati mai zuwa da ta kare hukumomin gwamnatin kasar  daga  abunda  ya  baiyana  na ‘Yan Siyasa  masu wuce gona da iri.