On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Karya Farashin Dala

Engr Sani Bala Tsanyawa

Dan Majalisar wakilai na Ghari da Tsanyawa Engr. Sani Bala Tsanyawa ya ce Karya Farashin Dala shi ne mafita domin samar da masalaha ga yan Kasa.

Injiniya Sani Bala Tsanyawa ya bukaci gwamnatin tarayya data karya farashin Dala domin samarwa da yan kasa saukin tsadar rayuwa.
 
Ya ce karya farashin Dala zai temaka wajen saukar farashin kayayyaki a kasar nan, Yana mai ra'ayin cewa koda samar da Dalar ne ga Yan canji daga ma'ajiyar Najeriya ta kasashen waje, zai temaka wajen samar da wadatuwar ta.

Engr Sani ya baiyana haka ne ya yin hirar da aka yi da shi a Arewa radio, Inda ya ce abunda ya kara asassa tashin Dala shi ne yawan dogara da kayayyakin kasashen waje da Yan Najeriya ke yi a maimakon amfani da na gida.