On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Ya Kamata Kasashe Su Dauki Matakan Dakile Bazuwar Cutar 'kyandar Biri.

KYANDAR Biri

Hukumar Lafiya ta duniya, tayi kira da a dauki matakan gaggawa domin dakile bazuwar cutar Kyandar Biri a nahiyar Turai, Inda ta baiyana cewa an samu rubunyar masu harbuwa da cutar a cikin makwanni biyu da suka gabata.

Tun a farkon watan Mayun Bana ne, aka samu fantsamar  cutar Kyandar Biri a  kasashe  yammacin Afrika da kuma na tsakiya , inda aka  fi samu  bazuwar ta.

Kaso 99 bisa 100  na gwaje-gwajen da aka yi sun tabbatar da cewa , mutane Dubu 4 da 500 da  suka kamu da cutar  sun fito ne daga nahiyar turai.

Bugu da kari a yanzu haka kasashe 31 aka samu rahoton cewa sun kamu da cutar.