On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Ya Kamata Shugaban Kasa Buhari Ya Mutunta Umarnin kotu, Inji Shugaban Jam'iyyar APC

SANATA ABDULLAHI ADAMU

Shugaban jam’iyyar APC na kasa,Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci shugaban kasa Muhammad Buhari da ya mutunta umarnin da kotun koli ta bayar kan batun canjin kudi.

Da yake yiwa manema Labarai a sakatariyar  jam’iyyar  dake  Abuja, Shugaban jam’iyyar, Ya  ce  wasu  manyan jami’an gwamnatin kasar nan guda ukku sun mutunta umarnin da kotun kolin ta bayar, domin rage  radadin da jama’ar kasa suke a ciki.

Bugu da kari  ya  ce  rashin martaba umarnin da kotun kolin ta bayar,  wata  babbar  tawaya ce   ga cigaban fannin   tattalin arzikin kasa.

Idan ba’a manta  ba, Kotun kolin ta  umarci  babban bankin kasa  da  kasa  ya fara aiwatar da tsarin  na dena  amfani da tsohon kudi a ranar  10 ga watan da muke ciki, har sai  zuwa lokacin da kotun zata kammala  sauraren shari’ar da aka shigar  gaban ta,  To sai dai  Shugaban kasa  Buhari da kuma babban bankin kasar  sun bijirewa  wannan umarni.