On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Yadda Al-ummar Garin Rummawa Suka Rabauta Da Makarantar Firamare Bayan Shekara Hudu Suna Amfani Da Makarantar Kara A Jihar Kano

Al’ummar  garin Rumawa dake karamar hukumar Ungoggo ta nan jihar Kano  na  matukar  farin ciki a saboda gina musu sabuwar Makarantar Firamare a yankin da aka yi, bayan shafe  tsawon shekara  hudu da  wata  guguwahade da Iska  ta yi awon gaba da   ginin makarantarsu da aka yi ta  da kara.

A halin yanzu dalibai na yin tururuwa  zuwa  makarantar  wadda a baya  suke karatu cikinta cikikin yanayi na takura, a  sakamakon  lalacewar da makarantar  tasu tayi, kafin majalisar karamar hukumar  Ungoggo ta kai musu dauki.

A  saboda  haka rahotonmu na musamman a wannan makon, Da wakilinmu Victor  Chiristopher  ya hada mana, hadin gwiwa da kungiyar  Nigeria Health Watch, Yayi duba kan  wannan  gagarumin tallafi  da Al’ummar garin Rumawa  suka samu, da kuma bukatar dake akwai ga sauran kananan hukumomi  su dauki darasi.

Saurari cikakken Rahoton da Kamaluddeen Muhammad ya karanta.