On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Yadda Al-ummar Unguwar Daurawa Ke Yiwa Kansu Maganin Barazanar Tsaro A Kano

Cikin wasu ‘yan shekaru da suka gabata,Unguwar Daurawa dake karamar hukumar Tarauni a jihar Kano ta kasance cikin yankuna dake daukar hankali kan kalubalen tsaro da ake fuskanta na cikin al’umma.

Wannan ne ya sanya aka kafa kungiyar ci gaban al’ummar Daurawa domin ceto mazauna yankin daga barazanar tsaro, kuma tun daga lokacin akayi nasarar shawo kan mummunar matsalar.

A yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa  tare da barazanar tsaro da aka saba na bibiyar zabuka,  Wakilinmu Nura Haruna Mudi yayi nazari akan kokarin da kungiyar tayi da kuma bukatar sauran masu ruwa da tsaki su yi koyi.

Saurari Kamaduludeen Muhammad da cigaban Rahoton: