On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Yadda Cibiyar CHRICED Ta Kawo Sauyi Ga 'Dabi'ar Rashin Kyale Mata Masu Juna Biyu Zuwa Asibiti A Jihar Kano

Da  yawa-yawan maza basa damuwa  da kai  matansu  asibiti a  lokacin da suke da juna biyu,  musamman a  yankunan karkara  na jihar Kano, Alamarin da ke haifar da  karin mace macen mata masu  juna  biyu da kanan  yara  a  jihar.

Wannan al’amari  baya rasa nasaba da tasirin al’ada da karancin likitocin mata da ake da su dama kudin da ake kashewa  ta  bangaren kula da lafiya, sai kudin mota da karancin wayar da kan al’umma, wanda  hakan ke cigaba da kawo babban nakasu  ta bangaren haihuwa a Asibitoci.
 

A kan haka ne rahotonmu na musamman a wannan makon, da wakilimu Victor Chiristopher ya hada mana , yayi duba kan irin gudunmuwar da  cibiyar   CHRICED  hadin gwiwa da wata kungiya mai rajin inganta fannin lafiya ta Health Watch ke bayarwa a wannan fannin domin ganin an samu sauyin da ake bukata.

Saurari Cikakken Rahoton.