On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Yadda 'Yan Kauyen Mutunji Na Jihar Zamfara Suka Mutu Saboda Yunwa A Hannun 'Yan Bindiga

Kwanaki ashirin da biyar bayan sace wasu mutanen kauye 150 a gundumar Mutunji dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, uku daga cikin wadanda al’amarin ya shafa sun mutu saboda yunwa yayin da 'yan fashin daji suka yi shiru kan batun kudin fansar sauran Mutane 147.

Idan ba a manta ba a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba na  2023 ‘yan bindigar suka kai hari kauyuka shida a gundumar Mutunji inda suka yi awon gaba da mutane 150 saboda gazawar su na biyan harajin Naira miliyan 200 da shugaban ‘yan bindigar Damina ya dora musu.

Sai dai wani mazaunin garin ya shaida wa jaridar dailytrust  cewa mutane ukun da aka ruwaito sun mutu ta yiwu sun mutu ne saboda yunwa, yana mai cewa ’yan kungiyar da suka yi garkuwa da su suna karkashin jagorancin wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga ne, Damina, wanda ya shahara wajen cin zarafin wadanda suka yi garkuwa da su.

Mazauna garin ya ce jama’a sun koma yin addu’o’in neman taimakon Allah domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin.

Rundunar ‘yan sanda ba ta ce komai ba kan al’amarin a kwanakin nan.