On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Yakubu Dogara Ya Goyi Bayan Takarar Atiku Abubakar

YAKUBU DOGARA

Tawagar wata kungiyar jiga-jigan jam’iyyar APC karkashin tsohon kakakin majalisar wakilai, yakubu Dogara sun nuna goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, A zabe mai zuwa.

Tawagar  kungiyar  tuntuba ta jagororin Arewa, wadda ta hada Musulmi da kirista sun nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP , bayan da kwamitin ta na tsare-tsare  ya gabatar mata da rahoto a Abuja.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba ne  ya gabatar da  Rahoton mai dauke dasa hannun shugabansa, Hon Mohammed Kumaila da Sakatarensa Nunghe Kele SAN.