On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Bindiga Sun Halaka Mutane 38 A Jihar Nasarawa

YAN BINDIGA

Wasu ‘Yan bindiga da ba’a san ku su waye ba sun halaka mutane 38, wanda ya hada da kananan yara da kuma Mata a garin Taka Lafiya na karamar hukumar Karu, dake jihar Nasarawa.

Shaidun gani da ido sun fadawa  jaridar  daily  trust  cewar, al’amarin ya samo usuli  ne makwanni  biyu da suka gabata, Lokacin da wani Manomi  dake  a  yankin Gwanja  kusa  da  garin  nasu na Taka lafiya, Ya tuhumi wani makiyayi saboda  kyale  shanunsa  su  shiga  cikin gonarsa  da  ya yi sabuwar shuka  a cikinta.

A ranar  Alhamis din data  gabata ce, ‘yan bindigar suka kaddamar da harin inda suka halaka  mutane  hudu  a nan take, Sannan  kuma ranar  juma’a  aka sake kawo  Gawar mutane  Bakwai  daga  garin na Takalafiya da sauran wasu garuruwa,  Inda aka kaisu  wurin ajiyar  gawa  na cibiyar  Lafiya  ta taraiyya dake  birnin Keffi, yayin da har  yanzu  ba’a  ga mutanen  yankin da dama  ba.

A ranar  Asabar ne  aka yi jana’izar  mutane  38 da  ‘yan bindigar  suka  halaka a garuruwan  biyu, Mataimakin gwamnan jihar, Dr  Emmanuel  Akabe  wanda  ya  jagoranci  tawagar jami’an gwamnati, wajen binne  mamatan,  yayi  tir  da kisan gillar da aka yiwa  mutanen.

Kazalikaya bada tabbacin cewar gwamnati zata bada tallafi  ga wadanda  aka raba da muhallansu,Sannan kuma ya bukace  su  dasu  temakawa  hukumomi  da  bayanan  da suka  dace.